ABNA24 : Kakakin Majalisar fayyace masalahar tsarin musulunci ta Iran, Muhsin Rizai ya bayyana cewa; Bayan cin amanar da mahukuntan kasar Bahrain su ka yi wa al’ummar musulmi na kulla alaka da ‘yan sahayoniya, mulkinsu ba zai dore ba.
Muhsin Rizari wanda ya wallafa sako a shafinsa na Twitter ya yi tir da yadda mahukuntan na kasar ta Baharain su ke kulla alaka da ‘yan sahayoniya.
Sakataren majalisar fayyace maslahar tsarin musulunci ta Iran ya kara da cewa; Kulla alaka da ‘yan sahayoniya da wasu kasashen larabawa su ke yi, sun yi wa Trump hidima ne da bashi kyautar jinin palasdinawa, sannan kuma da sarar al’ummar Palasdinu da wuka ta baya.
342/