14 Yuli 2020 - 14:04
Yamen: Hare-haren Da Mu ka Kai Wa Saudiyya Sun Yi Musu Asara Mai Yawa Ta Dukiya Da Rayukan Sojoji

Mataimakin shugaban gwamantin kasar Yemen a birnin Sanaa, janar Jalal al-Rawishan ya ce; Harin da dakarun kasar su ka kai da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuki a cikin Saudiyya sun sami cibiyoyin soja kuma sun haddasa asara ta dukiya da rayuka na gwamman sojoji daga cikinsu hadda kwamandoji.

(ABNA24.com) Janar al-Rawishan ya kuma ce; Tsarin yakin da su ke da shi na mayar da martani yana tafiya daidai, kuma yana cimma manufar da aka shirya.

A nashi gefen, mataimakin shugaban bangaren wayar da kai a ma’aikatar tsaron sojan kasar ta Yemen, kanar Abdullah Bin Amir, ya ce; Harin da su ka kai tsararre ne, kuma ba akai shi akan fararen hula ba.

A shekaran jiya Lahadi ne dai sojojin kasar ta Yemen su ka kai hare-haren daukar fansa akan cibiyoyin sojan Saudiyya a yankuna Jzan, Najran da Asir.

342/