7 Yuli 2020 - 13:05
Shugaban Brazil Ya Ce Yana Jin Alamun Covid-19 A Jikinsa

Shugaban kasar Brazil, Jair Bolsonaro, ya sanar da cewa yana jin wasu alamun cutar korona a jikinsa, wanda hakan ya sanya shi yin gwajin cutar.

(ABNA24.com)  Shugaban ya kuma shaidawa magoya bayansa cewa an duba masa huhunsa, kuma babu wata matsala a halin yanzu.

Dan shekaru 65, shugaba Bolsonaro, ana zarginsa da sakaci kan annobar ta korona, kuma na sha nuno shi a cikin jama’a baya sanye da takunkumin rufe baki da hanci, tare kuma da sukan matakan da wasu yankunan kasarsa ke dauka domin dakile yaduwar cutar.

Ko a jiya Litini, ya sake hawa kujerar na ki kan wasu kudurorin doka guda biyu na cilasta wa jama’a sanya takunkumi a wuraren dake fusknatar cinkoson jama’a.

Brazil, dai ita ce kasa ta biyu, bayan Amurka inda cutar ta fin illah a duniya, inda alkalumman baya bayan nan ke cewa mutum miliyan 1,6 cutar ta harba, yayin da kuma ta kashe mutum sama da dubu 65.

342/