(ABNA24.com) Ministan cikin gidan ƙasar Aly Ngouille Ndiaye ne ya sanar da hakan a yau ɗin cikin wani jawabi da yayi ta gidan talabijin inda ya ce daga yau za mu ɗage takunkumin zirga-zirga a duk faɗin ƙasar nan sai dai kuma dokar hana zirga-zirga daga ƙarfe 11 na dare zuwa 5 na safe za ta ci gaba da wanzuwa.
Al’ummar ƙasar Senegal ɗin dai suna ci gaba da nuna rashin amincewarsu da tsauraran matakan da gwamnatin ta ɗauka tun watan Maris ɗin da ya gabata wanda ya ƙara sanya mutanen ƙasar cikin halin tsaka mai wuya waɗanda mafiya yawansu suna fama da matsanancin talauci.
Cikin ‘yan kwanakin nan dai babban birnin kasar Dakar da sauran birane sun shaida zanga-zangar mutane masu nuna rashin amincewa lamarin da ya tilasta wa gwamnatin daukar wannan mataki na sassauci a yau.
342/