(ABNA24.com) Batun bawa firai ministan kasar Lesotho rigar kariya daga gurfana a gaban kotu bayan saukarsa daga mukaminsa a ranar 22 ga watan da muke ciki baya daga cikin batutuwan da aka tattauna a majalisar dokokin kasar a jiya Litinin.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa a jiya Litinin ce jam’iyyun da suka yi kawance da jam’iyyar Firai ministan kasar Thomas Thabane, sun fice daga kawancen nasu, wanda hakan ya tilastawa firai ministan sauka daga mukaminsa a ranar 22 ga watan mayun da muke ciki.
Wani mai Magana da yawun jam’iyyar “Democratic Congress party” Montoeli Masoetsa ya fadawa reuters cewa batun bashi rigar kariya daga gurfana a gaban kotu kan zargin kashe matarsa ta farko, idan ya sauka daga mukaminsa, baya daga cikin batutuwan da aka tattauna kafin a tilasta masa sauka kan mukaminsa.
Batun kissan matar firai ministan kasar ta Lesotho ta farko dai, ya jefa kasar cikin rikicin siyasa wanda ya sa ‘yan siyasa suka bukaci ya sauka kan mukaminsa, har sai kotu ta wanke shi.
An kashe matar Thomas Thabane ta farko ne ta harbi da bindiga kwanaki biyu kacal kafin a rantsar da shi a matsyin firai ministan kasar.
/129
13 Mayu 2020 - 06:20
News ID: 1036347

Batun bawa firai ministan kasar Lesotho rigar kariya daga gurfana a gaban kotu bayan saukarsa daga mukaminsa a ranar 22 ga watan da muke ciki baya daga cikin batutuwan da aka tattauna a majalisar dokokin kasar a jiya Litinin.