(ABNA24.com) Ma’aikatar kiwon lafiya ta Iran ta bakin kakakinta ce ta sanar da alkaluman wadanda su ka kamu da kuma rasuwa daga cutar ta corona a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata, wanda ya ke nuni da samun koma baya idan aka kwatanta da yadda ta kasance a baya.
Kakakin ma’aikatar kiwon lafiya ta Iran Kianush Jahanpur ya bayyana cewa; Adadin wadanda su ka kamu da cutar a cikin sa’o’i, 24 da su ka gabata, sun kai dubu daya da dari biyar da ashirin da tara.
Hakan ya kawo jumillar adadin wadanda su ka kamu da cutar sun kai dubu dari da shida, da dari biyu da ashirin, yayin da wadanda su ka mutu kuwa su ka kai 48.
Daga bullar cutar zuwa yanzu adadin wadanda cutar ta kashe a cikin kasar sun kai 6,589.
Kakakin ma’aikatar kiwon lafiyar na Iran ya kara da cewa; Ya zuwa yanzu adadin wadanda su ka warke daga cutar sun kai dubu 85 da 64.
/129
10 Mayu 2020 - 05:18
News ID: 1035222

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Iran ta bakin kakakinta ce ta sanar da alkaluman wadanda su ka kamu da kuma rasuwa daga cutar ta corona a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata, wanda ya ke nuni da samun koma baya idan aka kwatanta da yadda ta kasance a baya.