7 Mayu 2020 - 04:31
Iran : Amurka Ta Yi Wauta Da Ta Fice Daga Yarjejeniyar Nukiliya

Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta bayyana ficewar da Amurka ta yi a cikin yarjejeniyar nukiliya da wauta.

(ABNA24.com) Da yake bayyana hakan shugaban kasar ta Iran, Hassan Rohani, Amurka ta tafka wawan kuskure data yi watsi da yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran a shekara 2015, kuma abu guda wanda Amurka ya kamata ta yi yanzu ta gyara wannan kuskuren shi ne ta sake komawa a cikin wannan yarjejeniyar, inshi shi.

M. Ruhani, ya kuma ja kunnen sauren bangarorin da suka rage a yarjejeniyar akan duk wani yunkuri na tsawaita takunkumin cinikin makamai ga Iran.

A baya baya nan dai bayanai sun nuna cewa, mahukuntan Washington, na matsin lamba wa kasashen Jamus, Faransa da kuma Biritaniya, domin ta samu amincewarsu kan tsawaita dokar takunkumin kasa da kasa na sayar wa Iran makamai.

Dama kafin hakan sakataren majalisar koli ta tsaron kasa a Iran, Ali Chamkhani, ya shalanat cewa tsawaita takunkumin cinikin makamai kan Iran, tamakar kawo karshen abunda ya rage ne daga yarjejeniyar nukiliyar.

Takunkumin cinikin makaman wanda ya kamata a fara janyewa Iran a watan Oktoba mai zuwa, yana kunshe ne a kudiri mai lamba 2231 na kwamitin tsaron MDD, wanda kuma wani bangare na yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da Iran, wacce kuma shugaba Donald Trump na Amurka, ya yi, fatali da ita a shekara 2018, tare da sake kakaba jerin takunkuman tattalin arziki kan kasar ta Iran.

Bayanai sun ce Amurka na son yin amfani da wata hanya ta cewa har yanzu tana cikin yarjejeniyar domin cimma manufarta.


/129