Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti-ABNA24- ta nakalto Shugaba Rauhani ya bayyana haka ne yau a lokacin yake gabatar da wani jawabi a gaban wani taro da aka gudanar a birnin Tehran a yau Litinin, tare da jami’an gwamnatocin lardunan kasar.
Shugaban na Iran ya bayyana cewa; karfin soji yana matukar tasiri a cikin lamurran siyasar duniya a halin yanzu, wanda kuma Iran tana alfahari da ci gaban da ta samu a wannan bangare tare da taimakon Allah, da kuma himmar masana na kasar.
Ya ce amma abin da yake shi ne sirrin nasara, kuma dukkanin karfi yana tattare da hakan shi ne dogaro da Allah, da kuma amincewar jama’a da tsarin da ke tafiyar da lamarinsu, ta yadda za su iya yin sadaukarwa a kansa a dukkanin bangarori, ba kawai a bangaren jihadi na makami ba.
Dangane da dambarwa ta siyasa da ke cikin batun yarjejeniyar nukiliya kuwa, Rauhani ya bayyana cewa Iran ta yi aiki da dukkanin abubuwan da ta ratabbata hannu a kansu a cikin yarjejeiyar, amma Amurka ce ta sanya kafa ta yi fatali da yarjejeniyar, yanzu lamarin ya rage a hannu kasashen turai, ko dai su zabi zama masu ‘yancin siyasa kan wannan batu, ko kuma ‘yan amshin shata ga Amurka.