27 Janairu 2020 - 06:51
Iran Ta Yi Tir Da Cin Zarafin ‘Yan Kasarta A Amurka

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Abbas Musawi ya bayyana cin zarafin Iraniyawa a filayen saukar jiragen sama a kasar Amurka da ake yi, ya sabawa ka’ida ta kasa da kasa.

(ABNA24.com) A zantawarsa da manema labarai a nan birnin Tehran, Abbas Musawi ya bayyana cewa, irin matakan da jami’an tsaron Amurka suke dauka kan ‘yankasar Iran a kasar ta Amurka ba dai-dai bane, hakan ya yi hannun riga da dukkan ka’idoji da dokokin kasa da kasa.

Musawi ya ce baya ga haka kuma, wannan halin cin zarafin biladama ne, domin kuwa dukkanin mutanen da ake cin zarafinsu basu aikata wani laifi da ya sabawa wata doka a cikin kasarAmurka ba.

A kan haka ya ce yana kira ga mahukuntan Amurka da su gaggauta kawo karshen irin wannan dabi’a wacce ta sabawa ‘yan-adamtaka.

Haka nan kuma ya bayyana cewa zasu bi matakai na gaba domin bin kadin lamarin ‘yankasar ta Iran da ake ci zarafinsu a kasar Amurka ta hanyoyi na doka.




/129