Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti{a.s}ABNA-ta rawaito cewa :Benjamin Babban Kotun koli ta Nuremberg ya rubuta a cikin wata Makala cewa: kisan Laftanar Kanal Kassim Sulemani da umarnin Trump da sojojin Amurka suka yi a Iraki ana daukar shi a matsayin aikin fasikanci.Benjamin yace Yanzu, shekara ta dari, bazan iya yin shuru ba. Na zo Amurka ne a matsayina na dan gudun hijira . Ina jin nauyina ne in shigar da imanin na ga Amurkawana fada masu gaskiya.Ya kara da cewa :na halarci Yaƙin Duniya na II a matsayin sojan Amurka a fagen fama, kuma aka karrama ni da na yi aiki a Kotun manyan laifuka ta Nuremberg a matsayin babban mai gabatar.Ya kara da cewa: Mutane suna da hakkin sanin gaskiya. Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya, Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da Kotun Duniya ta Hague duk an keta su.Wata majiya a Amurka ta nakalto cewa kotun kasa da kasa mai hukunta manyan laifuka{ICC} za ta fitar da bayani na karshe kan Amurka bayan da kasar Iran ta shigar da kara a gaban kotun akan kisan shahid Kassim Sulemani.