Shugaban Najeriya ya umarci sojoji da hukumomin tsaro su ƙaddamar da wani aiki na gaggawa don ceto wadanda aka sace a jihar Nijar, a daidai lokacin da rundunar sojin Amurka a Afirka ta bayyana cikakken bayani game da atisayen soji na hadin gwiwa a Bauchi
An sace masu salla sama da 60 a harin da wasu mutane dauke da makamai suka kai kan babban masallacin garin Dakara a jihar Neja ta Najeriya. Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da ake gudanar da sallar Juma'a, kuma maharan bayan sun yi ta harbe-harbe kwatsam, suka fitar da wasu masu salla daga masallacin suka tafi da su zuwa daji.
Hukumomin Najeriya sun bayyana a jiya Litinin cewa 'yan bindiga sun sace akalla ɗalibai 39 da malamai bakwai a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya, suka kashe daya daga cikin malaman, tare da raunata jami'an tsaro ta hanyar amfani da bama-bamai a lokacin ƙoƙarin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.