Babban Darakta na cibiyar "Rosatom" ta Rasha kan makamashin atom, Alexei Likhachev, ya bayyana cewa cibiyar na shirin ƙara yawan ma'aikatanta a tashar wutar lantarki ta nukiliya ta "Bushehr" a Iran zuwa ƙwararru 200.
Babban manajan Rosatom ya sanar da fara sake aike da ƙwararrun wannan kamfani zuwa tashar nukiliya ta Bushehr, kuma ya bayyana cewa mutum biyar na farko sun isa wurin, kuma har zuwa lokacin kaka adadin ma'aikatan Rasha zai ƙaru zuwa 100.