Babban Sakataren Kungiyar Hizbullah, Sheikh Naim Qassem, ya tabbatar a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Al-Manar cewa Hizbullah tana wakiltar wani aiki mai mahimmanci ne wanda aka gina bisa hangen nesa mai haske don magance matsalolin 'yan kasa da kuma mayar da martani ga kalubalen da suke fuskanta, na zamantakewa ne ko na tattalin arziki ko na ilimi, ko kuma na alaka da ta’addanci da kwacewurare. Ya jaddada cewa Kungiyar tana daukar matsayi bayyanannu wajen fuskantar duk wani kalubale da ya shafi hakkoki da batutuwa na asali.