Mai magana da yawun harkokin fursunoni na Bahrain, yayin da ya ke sukar shari'ar malaman kasar, ya bayyana wannan tsari a matsayin wani ɓangare na matsin lamba na siyasa da zamantakewa a kan malamai da al'ummar Shi'a.
Gwamnatin Al Khalifa a Bahrain ta ƙara tsananta zalunci akan 'yan Shi'a a ƙasar, inda ta haramta musu tafiya zuwa Iran da Iraki, tana mai kwace waqafin dukiyar mabiya mazhabar Ja'fari, kuma tana kame malaman addini da shugabannin 'yan Shi'a.