Kusan babu wata jiha da ba a samu tangarda ba, kuma kusan duk suna kukan tilasta bin wani dan takara.
A jihar Katsina ma an tarar da wadannan matsaloli, wadanda har suka sanya sauran 'yan takarar gwamnan a zaben fidda gwanin suka fice cikin fushi daga dandalin zaben.
Cikin 'yan takarar dai har da tsohon mataimakin Marigayi Ummaru Musa 'yar adaua a lokacin yana gwamnan Katsina.
Alhaji Tukur Ahmed Jikamshin a tattaunawar mu da shi, ya bayyana cewar ko kusa ba a nuna adalci ba a zaben, don haka su, a wurinsu ba a yi zaben fidda gwanin takara ba na jam'iyyar ta PDP a Katsina.ABNA