Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, a cikin ziyarar da Ayatullah Ramezani ya kai nahiyar Afirka, babban sakataren majalisar duniya na Ahlul-baiti (AS) ya ziyarci asibitin kula da lafiya na kasar Iran da ke birnin Nairobi babban birnin kasar Kenya.
Dr. Faqihi, wakilin Iran a wannan asibitin, ya kuma yi bayani game da hidima da ayyukan jinya a wannan asibitin.
Yayin da yake yabawa ayyukan jin kai na wannan asibitin, Ayatullah Ramezani ya ce: Kenya za ta iya zama cibiyar kula da lafiya a nahiyar Afirka.



