(ABNA24.com) Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, Salam Al-shummari dan majalisar dokokin kasar Iraki a bangaren Sadr ya bayyana cewa, ‘yan majalisar dokokin Iraki a bangaren Sadr sun nuna goyon bayansu ga nada Kazimi a matsayin firayi ministan kasar Iraki.
Ya ce dukkanin ‘yan majalisar a bangaren gunguna magoya bayan Sadr, za su mara wa Alkazimi baya domin samun nasara wajen kafa majalisar ministoci.
Haka nan kuma ya kara da cewa, matukar dai Alkazimi ya yi aiki da alkawullan da ya dauka, kuma ya fifita maslahar kasar Iraki akan matsin lamba na manyan kasashen duniya, to kuwa zai ci gaba da samun goyon bayansu.
/129