22 Agusta 2019 - 06:00
Musulmi Ahlu Sunnah Sun Halarci Taron Ghadir A Bosnia

Bangaren kasa da kasa, musulmi ahlu sunna da dama ne suka halarci tarukan Ghadir da aka gudanar a birane daban-daban na kasar Bosnia.

(ABNA24.com) Bangaren kasa da kasa, musulmi ahlu sunna da dama ne suka halarci tarukan Ghadir da aka gudanar a birane daban-daban na kasar Bosnia.

Musulmi ahlu sunna da dama ne suka halarci tarukan da aka gudana na Ghadir a biranen Sarayevo, Visoko da Traunik da sauransua  kasar Bornia.

Wadanda suka gabatar da bayanai a wuraren tarukan sun mayar da hankali ne dangane da matsayin wannan rana da kuma gagarumin lamarin da ya faru a cikinta, wada yake a matsayin cikon addini.

Taron Ghadir na wannan shekara  akasar Bosnia ya dauki sabon salo da ba a saba gani ba, inda mabiyar mazhabar ahlul bait ne suka saba halartar wannan taro, amma a shekarar bana har da ahlu sunna.

Wannan lamari ya nuni da cewa batun Ghadir ba na wani bangare ba ne na musulmi, lamari na dukkanin al'ummar musulmi baki daya.




/129