15 Afirilu 2026 - 23:11
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Kai Hari Da Jirgi Maras Matuƙi Kan Ma'aikatan Ɗauki A Lebonan

Isra'ila ta kai wani hari da jirgin sama mara matuki a kan ma'aikatan agaji a kudancin Lebanon

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Isra'ila ta sake kai hari kan kungiyoyin ceto a kudancin Lebanon inda ta kai hari kan motocin daukar marasa lafiya a Miyfdun, duk da akwai bayyanar alamun ma'aikun daukin.

Jaridar Al-Akhbar ta kasar Lebanon ta ba da rahoton cewa masu ceto biyu sun yi shahada, wasu hudu kuma sun jikkata a wani harin da jirgin sama mara matuki ya kai kan wata motar daukar marasa lafiya a garin Meyfdun da ke Nabɗiyya.

Bayan yaɗa wannan labarin, kafofin yada labaran Lebanon sun ba da rahoton cewa wani jirgin sama mara matuki na Isra'ila ya kai hari kan wata mota a yankin da ke tsakanin Abel al-Saqi da Blat kusa da cibiyar Unifil.

Al'ummar Lebanon sama da dubu 9,000 ne kai shahada tare da raunukan a hare-haren Isra'ila kamar yadda Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta sanar da cewa mutane 2167 sun yi shahada kuma mutane 7061 sun jikkata a hare-haren ta'addacin Isra'ila a sassa daban-daban na kasar tun daga ranar 2 ga Maris (11 ga Maris).

…………………

Your Comment

You are replying to: .
captcha