14 Afirilu 2026 - 17:33
Source: ABNA24
Iran Ta Nemi Biyan Diyya Daga Ƙasashe Biyar Na Larabawa

Iran ta haka ta nemi diyya a hukumance daga Bahrain, Saudi Arabia, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Jordan, inda ta zarge su da haɗin kai wajen hare-haren Amurka da Isra'ila ta hanyar ba da damar yin amfani da sararin samaniya, sansanonin yanki. Tehran na neman cikakken diyya da aka kiyasta da ta kai dala biliyan 270.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: "Amir Saeed Irvani", jakada kuma wakilin dindindin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, ya nemi kasashe biyar na yankin, da su biya diyya sakamakon hare-haren da suka kai a Iran kasashen sun haɗa da Bahrain, Saudi Arabia, Qatar, UAE da Jordan, saboda sun shiga cikin Yakin Amurka da Isra'ila tayi akan Iran.

Ya kara da cewa: "Wadannan kasashe biyar, ta hanyar laifukansu na kasa da kasa, sun keta hakkin kasa da kasa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta haka ne zasu ɗauki nauyin alhakinsu na kasa da kasa, tare da "biyan asarar da suka haifar ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ga duk wani lahani na zahiri da na dabi'a saboda sun aikata laifukan ƙasa da ƙasa.

Iran ta haka ta nemi diyya a hukumance daga Bahrain, Saudi Arabia, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Jordan, inda ta zarge su da haɗin kai wajen hare-haren Amurka da Isra'ila ta hanyar ba da damar yin amfani da sararin samaniya, sansanonin yanki. Tehran na neman cikakken diyya da aka kiyasta da ta kai dala biliyan 270.

Your Comment

You are replying to: .
captcha