12 Afirilu 2026 - 11:40
Source: ABNA24
Amurka Ta Yi Asarar Jiragen Sama Marasa Matuƙa 24 Nau'in MQ-9 A Yaƙinta Da Iran

Rundunar sojin Amurka ta yi asarar jiragen sama marasa matuka na MQ-9 Reaper guda takwas tun farkon watan Afrilu yayin hare-haren da suke kaiwa Iran

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Rahoton ya bayyana cewa jimillar asarar wannan samfurin jirgin mara matuki tun lokacin da aka fara yakin a ranar 24 ga Maris ya kai dala miliyan 720, inda kowane MQ-9 ya ci kusan dala miliyan 30 ko fiye. Majiyoyin Iran sun kuma ba da faɗi cewa har walayau jirgin MQ-4C Triton na leken asiri, wanda darajarsa ta kai kusan dala miliyan 250, ya bace ko na dai Iran ta kakkaɓo shi.

Your Comment

You are replying to: .
captcha