12 Afirilu 2026 - 10:54
Source: ABNA24
Baqa'i: Saɓani Akan Batutuwa 3 Su Suka Hana Kaiwa Ga Fahimtar Juna

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran: "Mun tattauna batutuwa 10 na Iran da batutuwan bangaren Amurka". 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Ismail Baqa'i a bayaninsa da ya yi, a safiyar yau Lahadi ya ce "Mun tattauna batu 10 na Iran da kuma batutuwan bangaren Amurka kuma bangarorin biyu sun cimma fahimta kan wasu batutuwa da dama, amma an samu gibi a wasu ra'ayoyi kan muhimman batutuwa 2-3, kuma a karshe tattaunawar ba ta kai ga cimma yarjejeniya ba, ya kara da cewa "hanyar diflomasiyya ba a rufe ta ke ba. Hanya ce ta dindindin don kiyaye muradunmu na kasa "Diplomasiyya ba za ta ƙare ba kuma kayan aiki ce don kare muradun ƙasa.
Dole ne jami'an diflomasiyya su yi aikinsu, a lokacin yaƙi ko kuma lokacin zaman lafiya, "in ji shi, yana mai tunawa da cewa an yi wannan tattaunawar kwanaki 40 bayan yaƙin da aka yi, kuma a cikin yanayi na rashin yarda da mummunan zato; A dabi'ance dama ta yiwuwa ba za muyi tsammanin a cimma yarjejeniya a cikin zama ɗaya. 
Kuma babu wanda ya yi tsammanin hakan. “Sauran batu shi ne sarkakiyar al’amura da yanayi. Wasu sabbin batutuwa, kamar mashigar Hurmuz, an kara su cikin wadannan tattaunawa, kuma kowannensu yana da nasa sarkakiyar.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada: Diflomasiya tana nan tare da masu kare mahaifarsu, kuma a shirye muke mu yi duk wata sadaukarwa.
Sannan yayi godiya ga Pakistan: Ina mika godiya ga gwamnati da al'ummar Pakistan, musamman ga Mista Shahbaz Sharif, Firayim Minista na Pakistan, da Mista Asim Mounir. Kwamandan rundunar ƙasar, da Sayyid Ishaq Dar, mataimakin firaminista. Muna gode musu da kyakkyawar karbar bakuncinsu, kuma muna da yakinin cewa za a ci gaba da hulda tsakaninmu da Pakistan da dukkan abokanmu na yankin. 
Diflomasiya tana nan tare da masu kare ƙasarsu, kuma a shirye muke ga kowace sadaukarwa.

Your Comment

You are replying to: .
captcha