Cikakkun bayanai game da hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kai kan manyan cibiyoyin man fetur na Amurka a yankin. A cikin hare-haren an kai hari ga wasu manyan cibiyoyi guda biyu na kamfanonin Amurka a Saudi Arabia:
1- Katafaren cibiyar petrochemical a yankin Al-Jubeil, Saudi Arabia, wanda yake na kamfanonin Amurka ne "Sadra", "Exon. Mobil" da "Darkmikal", sun lalace sosai ta dalilin harin makamai masu linzami da Jirage marasa matuka.
2. Rukunin man petrochemical na kamfanin Amurka "Shorden Phillips" da ke yankin Al-Jaima na Saudiyya shi ma an hare da shi da makamai masu linzami masu gajeren zango jiragen sama marasa matuka na dakarun juyin juya halin Musulunci, inda harin yi wa cibiyoyin da kayayyakinsu mummunan lahani.
Yana da kyau a ambata cewa an kai wadannan hare-hare ne a matsayin martani ga hare-haren da makiya ke kai wa rukunin man fetur na Iran. Jaridar Wall Street Journal ta nakalto wasu majiyoyi na cewa, asarar kudaden da ake yi wa tattalin arzikin Saudiyya dangane da asarar kudaden shiga da kuma karin kudaden ta dalilin harin da Amurka ke yi kan Iran ya haura dala biliyan 10.
Your Comment