Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ofishin Hulɗar da Jama'a na IRGC: Bayan 'yan sa'o'i da suka gabata, an lalata makamai masu linzami na Tama Hawk guda biyar da makami mai linzami guda daya na Koroz a sararin lardin Qazvin. Sa'o'i da suka gabata, an lalata makaman ne ta hanyar amfani da sabbin na'urorin tsarin tsaron sama bisa buɗe wutar dakarun Hazrat Sahibil-Amr (AS) a sararin samaniyar lardin Qazvin.

Ana amfani da makami mai linzami na Tom Hawk mai nauyin kilogiram 500 don rushe ababen more rayuwa da kayan ma'aikatu wanda sojojin ruwan Amurka su ke amfani da shi musamman. Maƙiya sahyoniya da Amurka sun anfani da irin wannan makamin ne a harin da suka kai kan makarantar Minab wanda ya kashe ɗalibai mata 175 da wasu malaman makarantar.
IRGC, a matsayin dakaru masu karfi ƴaƴan al'ummar Iran, ta sanya lamarin hukunta masu zalunci a kan ajandarta, kuma ta hanyar dogaro ga Allah Madaukakin Sarki da goyon bayan jama'a, ta yi nuni da faruwar mummunan ranaku ga makiya, kuma sun sha alwashin cewa za su tunatar da abokan gaba game da martani mai tsanani a filin yaƙi.
Your Comment