Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: dakarun Iran sun aiwatar da matakin kai hari karo na 37 a jerin hare-haren ƴakin Wa'adi Sadigh 4 inda ta aike da manyan makamai masu linzami nau'i-nau'i i.
Ofishin hulɗar jama'a na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta sanar a cikin wata sanarwa cewa, a harinta karo na 37 a ƴakin wa'adi Sadigh 4 ta aike da manyan makamai masu linzami irinsu Khorramshahr da sauran makami mai linzami masu nauyi, wanda shine hari mafi nauyi da tsanani akan wuraren abokan gaba na Isra'ila da Amurka a cikin sa'o'i uku ajere.
A cikin sanarwar ofishin hulda da jama'a na jami'an tsaron juyin juya halin Musulunci, ya zo cewa an harba makaman ne bisa dogaro da ambaton sunan: "Ya Ali Ibn Abi Ɗalib As" a cikin dararen Layali Qadr daren shahadar Amirul Muminin (AS) tare da nau'ukan makamai masu nauyi akan wuraren Amurka da gwamnatin Sahayoniya.
A wannan karon sai biyu aka kai hari kan cibiyoyin setlite na Hayila na soji da cibiyoyin soji da ke Beer Yaqub, West Jerusalem da Haifa, tare da kai hare-haren kan wuraren Amurka da ke Erbil da sansanin sojin ruwa na biyar a yankin, dukkan wadannan wurare sun sha wuta daga makaman sojojin dakarun juyin juya halin Musulunci Iran. Allahn Musa da Haruna ya aike da wutar fushinsa a kan Fir'aunan wannan zamani.
Nasarorin da aka samu a wannan gagarumin hari da aka sadaukar da su ne ga ruhi mai tsarki na babban jagora da rayukan dukkan kwamandojin da suka yi shahada da daidaikun mutanen da suka yi shahada.
Muna ci gaba cikin kai hari mai hadafi da ƙarfi mai ci gaba, kuma a ci gaba da yaƙin, muna tunanin cikakken mika wuyan abokan gaba.
Za mu kawo karshen yakin lokacin da aka kawar da hatsarin yaki daga kan kasar. Har ila yau, ofishin hulda da jama'a na jami'an tsaron juyin juya hali sun sanar a wata sanarwa cewa, a ci gaba da gudanar da harin ayari na 37, na Wa'adi Sadigh 4 da yanzu kai albarka na: Ya Ali Ibn Abi Talib (AS), suna ci gaba da harba sabbin makamai masu linzami na Khorramshahr mai dauke da tan 2 a sansanonin sojojin ta'addancin Amurka da ke yankin.
Shi ma sansanin Amurka na Arifjan an harba masa makamai masu linzami guda biyu daga sashin makami mai linzami na ƙasa na IRGC.
Your Comment