Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sashen hulda da jama'a na Rundunar Sojojin Ruwa ta IRGC ya bayyana cewa atisayen, wanda ya fara a yau kuma zai dauki tsawon kwana biyu, zai gudana ne a Tekun Farisa, tsibirai uku, Mashigar Hormuz, da Tekun Oman. Kwamandan Rundunar Sojojin Ruwa ta IRGC Rear Admiral Ali Reza Tangsiri ya ce atisayen "Iqtidar" zai gwada tsarin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki a karkashin cikakken yanayin yakin fasahar lantarki.
Rundunar Sojojin Ruwa ta Iran ta sanar da cewa tana gudanar da atisayen sojojin ruwa mai taken Shahid Mohammad Nazeri a Tekun Farisa.
Your Comment