18 Nuwamba 2020 - 17:34
Hukumar Lafiya Ta Duniya Ta Yaba Wa Kasar Mozambique Akan Matakan Da Take Dauka Na Fada Da Cutar Corona

Hukumar lafiyar ta kasa da kasa ( W.H.O) ta kuma bayyana cewa matakan da ake dauka a kasar ta Mozambique sun taimaka wajen takawa yaduwar cutar birki.

ABNA24 : Daga bullar cutar ta Covid-19 zuwa yanzu adadin wadanda su ka kamu da ita, ba su wcue 14,000 ba, yayinda wadanda su ka rasu kuwa shi ne 115.

Wakilin hukumar kiwon lafiyar ta duniya a kasar ta Mozambique Tomas Valdez ya ce; tun daga bullar cutar a karon farko a kasar a ranar 22 ga watan Maris na wannan shekara ta 2020 aka fito da tsarin bin diddigin duk wanda ya kamu da cutar.”

Ana daukar tsauraran matakai a kasar ta Mozambique domin hana yin taruka. Har ila yau matakan da ake dauka sun hada tilastawa matuka motocin haya rufe fuskokinsu da kuma yin feshin kashe kwayoyin cutuka a ababen hawansu.

Gwamnatin kasar ta Mozambique ta bukaci kudaden da suka kai Euro miliyan 590 a farkon bullar cutar, ta kuwa yi amfani da su wajen wadata asibitocin kasar da kayan aiki, dakunan nazari da bincike sannan kuma kwararrun likitoci.

342/