29 Maris 2016 - 11:04
Kwamandan IRGC: Iran Ba Za Ta Dakatar Da Shirin Makamanta Masu Linzami Ba

Kwamandan dakarun kare sararin samaniyya na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Birgediya janar Amir Ali Hajizadeh ya bayyana cewar Iran ba za ta taba dakatar da karfafa karfin makamai masu linzaminta na kariya ba.

Birgediya Janar Hajizadeh ya bayyana hakan ne a matsayin mayar da martani ga ci gaba da barazanar da jami'an Amurka suke yi na kakabawa Iran takunkumi biyo bayan gwajin makamai masu linzami masu cin dogon zango da ta yi a kwanakin baya inda ya ce: A baya mun sanar da cewa koda za su gina katanga ne don killace Iran, (ba wai takunkumi kawai ba), to kuwa ba za a taba dakatar da kera makamai masu linzami a Iran ba", yana mai cewa Iran za ta mayar da martani ga duk wani kokarin wuce gona da iri a kanta.

Janar Hajizadeh ya sake jaddada cewar babu wani da yake shakku kan cewa Iran tana kera wadannan makamai ne don kare kanta daga duk wani wuce gona da iri da za a mata.

A ranar Alhamis din da ta gabata ce ma'aikatar kudi ta Amurka ta sanya takunkumi kan wasu kamfanoni guda biyu na Iran bisa cewa suna taimakawa shirin kasar na kera makamai masu linzami masu cin dogon zango; a ci gaba da kokarin Amurkan na takurawa Iran tun bayan gwajin wasu makamai masu linzami guda biyu da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar suka yi a wani atisayen soji da suka gudanar a kwanakin baya da aka ba shi sunan Eqtedar-e-Velayat.288