8 Afirilu 2025 - 08:55
Source: ABNA24
An Kori Jakadan Isra'ila Daga Taron Tarayyar Afirka

Mun yaba da matakin jajircewa da kungiyar Tarayyar Afirka ta dauka na korar jakadan Isra'ila daga taron da aka yi a babban birnin Habasha kan kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda. 

Kamfanin dillancin labaran kasa da kas ana Ahlul Bayt (As) – ABNA - ya habarta cewa: an kori jakadan Isra’ila a kasar Habasha daga hedkwatar kungiyar tarayyar Afrika, sakamakon adawa da kasashen da ke halartar taron na shekara-shekara suka nuna.

Kamfanin dillancin labaran ya bayar da rahoton cewa, Abraham Negus, jakadan Isra'ila a kasar Habasha, an kore shi daga dakin taro na Mandela da ke hedikwatar kungiyar tarayyar Afrika a ranar Litinin.

Korar jakadan ta zo ne bayan da wasu kasashen Afirka suka nuna adawa da halartar taron shekara shekara kan kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda.

Halartar jakadan yahudawan sahyoniya a wannan zauren ya kasance kwatsam. Wata majiyar diflomasiyya da ke halartar taron ta shaida cewa tawagogin kasashen Afirka da dama sun nuna rashin amincewarsu da zuwansa, kuma an dakatar da taron har sai da ya tafi.

Wakilin jarida sun rawaito cewa kungiyar Tarayyar Afirka na gudanar da bincike domin gano bangaren da ta gayyaci jakadan na Isra'ila.

A shekara ta 2002, bayan kafuwar kungiyar Tarayyar Afirka, kasashe da ba mambobi daga wajen nahiyar Afirka, wadanda adadinsu ya kai 87, aka ba su izinin zama mamba na sa idon.

Memba mai sa ido zai iya halartar tarurrukan Tarayyar Afirka kuma ya shiga wasu tattaunawa, amma ba shi da 'yancin kada kuri'a. Kasa ta farko da ta sami matsayin 'yan kallo ita ce kungiyar 'yantar da Falasdinu a shekara ta 1973, wacce ke samun gagarumin goyon baya daga galibin kasashen Afirka.

A shekarun baya-bayan nan dai Isra'ila ta nemi zama mamba a kungiyar Tarayyar Afirka don dakile tasirin Falasdinawa, kuma ta yi nasarar samun wakilcin 'yan kallo a shekara ta 2021. To sai dai daga bisani wani matakin da kasashen Afirka suka dauka na kore ta saboda saba ka'idojin Yarjejeniya Ta Tarayyar Afirka na amincewa da kasancewarta mamba a matsayin 'yar sa idon saboda ci gaba da mamaye yankunan Falasdinawa.

Kungiyar Hamas a na ta martanin ta ce: Korar jakadan Isra'ila daga taron Tarayyar Afirka mataki ne na tallafawa gwagwarmayar al'ummar Palasdinu.

Kungiyar gwagwarmayar Hamas ta sanar a cikin wata sanarwa cewa:

Mun yaba da matakin jajircewa da kungiyar Tarayyar Afirka ta dauka na korar jakadan Isra'ila daga taron da aka yi a babban birnin Habasha kan kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda. Matakin da ya dace da dabi'u da ka'idojin wannan kungiya da matsayinta na goyon bayan gwagwarmayar al'ummar Palastinu da kin 'yan mulkin mallaka.

Rashin kunyar gwamnatin Sahayoniya ya kai wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba, inda ta tura wakilinta zuwa taron bitar kisan kare dangi a yayin da sojojinta na dabbanci ke aiwatar da kisan gillar da ba a taba ganin irinsa ba a kan al'ummarmu a zirin Gaza.

Your Comment

You are replying to: .
captcha