03/Jumadassani/ 11/ Bayan Hijra
Wannan Rana Tana Daya Daga Ranekun Da Aka Ruyawaito Shahadar Sayyidah Fatimah As Kasancewar Matsalar Rubutu Da Aka Samu Wajen Rubuta Ranar Da Tayi Shahada Daga Ciki Akwai Wannan Rana Kamar Yadda Ruwayar Kwanaki 95 Ta Nuna.
Sayyida Zahra (As) ta kasance mai ilimi da mafi girman koyarwar mafi girma tun tana karama a karkashin jagorancin mahaifinta Manzon Allah (SAW). Ya kasance daya daga cikin abubuwan da Allah ya datar d ita shine amfana da yawa da tayi daga tushen ilimomin Ubangiji. Sayyida Zahra (AS) diyar Manzon Allah ce, matar Imam Ali As kuma Mahaifiya ga Imamai da Imamanci, kuma ita ce ta zamo mahada tsakanin Annabci da Imamanci. A tsawon rayuwarta Sayyidah Fatima Zahra (AS) ta kasance mai karamci, sadaukarwa, gafara, hakuri, gamsuwa, bautar Allah da taimakon talakawa ta hanya mafi kyawu, kuma ta tarbiyyanci Mutane masu Girma a tsawon Tarihi Kamar su Imam Hasan da Imam Husaini (as) sun samu tarbiya daga gareta sun tashi a hannunta. Sayyidah Fatimah As, bayan mahaifinta mai daraja, ita ce mutum na farko da ya fara haduwa da Mazon Allah SAWA daga gidan Bani Hashem. Sayyida Zahra (AS) a lokacin shahadarta tana da shekaru goma sha takwas kuma ta haifi ‘ya’ya hudu Imam Hasan da Imam Husaini (a.s) da Zainab da Ummu Kulthum (a.s).
Tun bayan wafatin Ma’aikin Allah SAWa Sayyada Fatimah As ta kasance tana yin kukan rashin maahaifinta manzon Rahama Sawa wanda har takai makotanta sunayin kuka duk lokacin da take yin kuka hakan abun ya zama kamar sarka idan tayi kuka mokatan acikin gidansu daya bayan daya suna amsa wannan kukan nata har wasu lokutan madina ta dauka da kuka gaba daya saboda Manzon rahama bai dade da wafati ba SAWA hakan ya sanya mutane suka zo wajen Imam suka kace Ali kayi wani abu da zai sanya Zahra tadan rage kukanta domin duk lokacin da tai kuka madina tana amsawa ne to Imam Ali Haka ya fadawa Sayyidah korafin mutanen Madina sai tace dashi ya samu wani waje a wajen madina ya kebance mata domin inason dani da yayana inje wajen gari inyi makokin mahaifina inyi kuka saboda rashin shi saboda banso insa ran mutane ya baci akan haka, haka kuwa akai Imam Ali As ya gina mata waje wanda shike kira da baitul Huzni takan je ta zauna tare da ‘yayanta suyi ta kuka. Wanda tun bayan wafatin mahaifinta fuskarta arufe take tana yin kuka tana kara damuwa da ramewa rana bayan rana har lokacin Shahadarta As.
05/Jumassani/656h
A Irin Wannan Rana Ne Dai "Ibn Abi Al-Hadid", Babban Malami Masanin Tauhidi, Fikihu Kuma Mai Sharhin Littafin Nahj Al-Balaghah Ya Rasu (656H).
An haife shi a birnin Madain Izzuddin Abu Hamid Abdul Hamid bn Hibbatul Allah wanda aka fi sani da Ibn Abil-Hadid, babban marubuci musulmai, masanin tauhidi, fikihu, mawaki kuma marubuci, a shekara ta 586 bayan hijira, Kuma yana dan goma sha biyar ya halarci karatuttukan fitattun malamai na Bagadaza na wannan zamani.. A Birnin Bagadaza, Ibn Abil Hadid ya dukufa wajen karanta littattafai da tara ilimi, kuma ya shiga cikin da'irorin adabi da na ilimmai masu yawa, ta yadda ya zama daya daga cikin malamai na lokacin. Ibn Abi al-Hadid ya kasance kwararre a fannin wakoki na dabi'a kuma yana karanta wakoki a fannoni daban-daban, amma wakokinsa na munajaty da addu'o'insa na sufanci sun fi shahara. An kama shi ne a lokacin da Mogol suka mamaye Bagadaza, amma an ‘yantar da shi ta hanyar shiga tsakani da wasu dattawan birnin sukai ta hakane har ya samu kubuta da daga mutuwa. Babban aiki na ilimi mafi shahara da Ibn Abi Al-Hadid yayi shine Sharhin Littafin Nahj al-Balaghah, wanda littafi ne dake dauke da tarin maganganun Imam Ali (AS). A cikin wannan littafi Ibn Abi Al-Hadid ya bayyana kuma ya gabatar da irin girman Nahjul Balagha ta fuskar adabi da tarihi da tauhidi. Duk da cewa dabi'ar Shi'anci tana da yawa a cikin sharhinsa na Nahjul Balagha, amma akwai abubuwan da ke cikinsa wajen sharhin su da ba su dace da akidar Shi'a gaba daya ba musamman game da mas'alolin Imamanci da ma'anonin tarihi masu alaka da wannan bangaren. Duk da cewa Ibn Abi al-Hadid ya tsira daga mutuwa a farmakin da Mogol suka yi wa Bagadaza ta hanyar ceton Khawaja Nasiru Dinud-Tusi da malaman Bagadaza, ba dadewa ya rasu a birni guda yana da shekaru saba'in.