2 Nuwamba 2024 - 05:57
Rahoton Taron Tunawa Da Sayyid Hashem Safiyyuddin Da Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Gudanar + Hotuna Da Bidiyo

An gudanar da taron tunawa da Sayyid Hashem Safiyyuddin a harabar Imam Khumaini (RA) da ke hubbaren Sayyidah Ma’sumah (a.s) a birnin Qum.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bait (As) - ABNA - ya habarta cewa: domin tunawa da girmama matsayin shahidi Hujjatul-Islam walmuslimin Sayyid Hashim Safoyyuddin shugaban majalisar zartarwa na kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da kuma girmama matsayin shahidai na tafarkin gwagwarmaya agba daya, an gudanar da taro bias daukar nuyin Majalisar Ahlul-baiti (A.S) ta duniya tare da halartar cibiyoyi masu alaka da juna a sashen Shabestan na Imam Khumaini (a.s) a hubbaren Sayyidah Ma’asumah (As) a birnin Kum.

A cikin wannan taro, Ayatullah Muhsin Qummi, mataimakin mai kula da harkokin sadarwa na kasa da kasa na ofishin Jagoran juyin juya halin Musulunci da Ayatullah Mahmud Muhammadi Iraqi da Ayatullah Riza Ramazani, babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (AS) da Ayatullah Sayyid Hashim Husaini Bushehri. Shugaban kungiyar malaman makarantar Qum, Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, mataimakin shugaban makarantar tauhidi ta Qum, Ayatullah Mahdi Shab Zindedar, memba na majalisar shari'ar da Hujjatul-Islam walmuslimin, Sayyid Ali Akbar Ajaqnejad, mai kula da masallacin Juma'a mai alfarma na Jamkaran. Hujjatul-Islam walmuslimin Ali Abbasi, shugaban jami'ar Al-Mustafa International University, Ayatullah Mahmud Rajabi, shugaban cibiyar ilimi kuma wani bincike na Imam Khumaini (a.s.), Ayatullah Abbas Kaabi, mamba a majalisar gudanarwa ta majalisar Kwararru a fannin jagoranci, Ayatullah Najmudden Tabasi, memba na jami’ar madrasain Qum, Hujjatul-Islam walmuslimin, shugaban ofishin kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon a birnin Qum, da Sheikh Ghazi Hanina, shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar amintattun malamai na kasar Lebanon ne suka samu halarta.

Iyalan gidan shahidi Sayyid Hashim Safiyyuddin da wakilai daga manyan Maraji’ai da suka hada da ofishin Ayatullahi Makarem Shirazi da Ayatullah Nuri Hamdani da Ayatullahi Jawadi Amoli na daga cikin sauran mahalarta taron.

An fara gudanar da taron tunawa da shahid Sayyid Hashem Safiyyuddin da karatun kur'ani mai tsarki wanda makarancin kasa da kasa Muhammad Ali Foroughi ya gabatar, sannan kuma aka karanta sakon jagoran juyin juya halin musulunci bayan shahadar wannan fitaccen jami'in kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon.

Shahidi Hashim Safiyyuddin Babban Mujahid Ne

Ayatullah Riza Ramazani, babban sakataren majalisar Ahlul-baiti (AS) ta duniya wanda shine a matsayin mai jawabi na musamman a wannan taron, yayin da yake ishara da rayuwar shahid Sayyid Hashim Safiyyuddin ya bayyana cewa: Wannan shahidi ya kammala karatunsa na addini a makarantun hauza na birnin Qum da Najaf Ashraf kuma yana dan shekara 30 a duniya bisa gayyatar shahida Sayyid Hasan Nasrallah ya halarci kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon a matsayin mai fada a ji, kuma shahid Sayyid Hashim Safiyyuddin ya kasance mamba a majalisar shawara ta kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon yana da shekaru talatin da daya. Shi dai wannan shahidi ya rike mukamai daban-daban a kungiyar Hizbullah ta Labanon kuma ya kasance shugaban majalisar zartarwa ta Hizbullah ta Labanon na tsawon lokaci.

Ya ci gaba da cewa shahid Sayyid Hashim Safiyyuddin ya yi imani da jihadi da hadin kai a tsakanin kungiyoyin gwagwarmaya, ana daukar wannan shahidi a matsayin mujahidi a ma’anar hakikanin kalamr Mujahidi. Wata sifa ta shahid Sayyid Hashim Safiyyuddin ita ce yadda ya kasance mai ladabi da biyayya ga Ubangiji. Wannan shahidi ya yi kokarin kiyaye wadannan al'adu a cikin karatunsa da kuma mu'amalarsa da wasu. An dauki shahid Sayyid Hashim Safiyyuddin a matsayin wanda ya samu tarbiya daga Imaman juyin juya halin Musulunci guda biyu. Wannan shahidi ya yi imani da Wilayatul Faqih a tsantsar ma'anarsa. Ya dauki kansa a matsayin sojan makarantar wilaya kuma mai tasirantuwa daga jagoran juyin juya halin musulunci.

Babban shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) ta duniya a karshen bayaninsa yayi ishara da cewa: shahid Sayyid Hashim Safiyyuddin ya san wannan gwagwarmay tun yana matashi. Shi dai wannan shahidi ya kasance daya daga cikin jagororin gwagwarmaya, amma kuma ana ganinsa a matsayin mutum na kwarai. shahid Sayyid Hashim Safiyyuddin babban Mujahid ne kuma baya tsoron makiya. Yahudawan sahyoniya sun yi amfani da bama-bamai da dama wajen shahdantar da Shahidi Sayyid Hasan Nasrallah da shahid Sayyid Hashim Safiyyuddin. Amma abin da ke da muhimmanci shi ne cewa mazhabar Sayyid Hasan Nasrallah tana nan a raye kuma tana ci gaba da fadada kowace rana.

A karshen taron tunawa da shahid Sayyid Hashim Safiyyuddin ya kasance da yabon juyayi daga mawakin Ahlul Baiti (a.s) Haj Hasan Shalbafan.

Yana da kyau a lura cewa kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar da shahadar HujjatuIslam wal muslimin "Sayyid Hashim Safiyyuddin " shugaban majalisar zartarwar kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon a wani harin bam da yahudawan sahyuniya suka kai a yankunan kudancin birnin Beirut, babban birnin kasar Labanon da jiragen yakin gwamnatin Sahayoniya.