Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Mintuna kadan da bada umarnin ministan harkokin cikin gida aka fara gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na 14 a fadin kasar
Sunayen 'yan takarar zaben: "Masud Pizishkiyan - Mai Lamba 22"; "Mustafa Pourmohammadi - Mai lamba 33"; Sa'id Jalili Mai lamba 44"; "Muhammed Baƙhir Qalibaf - Mai lamba 77.
Hedikwatar Zabe ta Kasa: Za a yi zabe na tsawon sa'o'i 10, wanda za a iya tsawaita shi da hukuncin da ministan cikin gida ya yanke.
Hedikwatar zabe ta sanar da tsawaita lokacin kada kuri'a har zuwa karfe 08:00 na dare a fadin kasar.