Lokacin da Annabi Isma’il (AS) ya kai tsakiyar
shekaru, Allah Madaukaki ya umarci Annabi Ibrahim (AS) da ya sake zuwa Makka
daga Sham kuma tare da taimakon Isma’il (AS) ya sake gina dakin Allah.
Annabi Ibrahim (as) yace: ya Allah, a ina zamu gina ta? Sa wahayi ya sauka gareshi a daidai wurin da Adam (as)gaba ninka ya gina Kubba awajen.
Daga nan sai Malaika Jibrilu ya nuna wurin ga Annabi Ibrahim (as) kuma ya Kayyade masa iyakokinta da Bangarorinta sannan ya kawo tubalin asasinta daga Aljanna sannan Allah madaukakin sarki da dutse da farinsa yafi Kankara daga Aljanna zuwa ga Ibrahim (as) bayan sanya shi ajikin bangon Kabah yau da kullum saboda shafa da tabawar da Mushirkai suke masa ya zama baki har aka sanshi da Baƙin Dutsen.
Wanda lokacin ginin Annabi Isma’il yakasance yana dauko duwatsu daga dutsen Zi duwa yana kawo Annabi Mahaifnsa shi kuma yana Dorawa har saida ya kai zira’i tara na ginin sannan yasanya dutsen Hajril Aswad ajiki wajen da har yanzu yake dai bai canja ba, kuma yayi kofofi biyu ga dakin Kaabah daya abangaren Gabas daya kuma Yamma.
Bayan sun gama aikin ginin dakin Kabaah sai suka fara ziyartar sa Mala’ika Jibril a ranar 8 ga Zulhijja ya sauka gare su yace da Annabi Ibrahim As: Ya kai Ibrahim ka tashi ka tanadi ruwa, kasancewar a Minna da Arfat babu Ruwa saboda haka ake kiran ranar 8 gawatan zulhijjad da ranar tarwiyyah saboda a ranan aka umarceshi daya nemi Ruwan dazai wada ceshi.
Bayan nan Mala’ika Jibrail As yayiwa Annabi Ibarhim da Dan Sa Isma’il Jagora zuwa Munna Da Arafat ya koya musu Ayyukan Hajji kamar yadda ya koyawa Annabi Adam As kafin nan.
A cikin Alkur’ani mai Girma Ayoyi da dama sunyi bayanin dangane da haka daga cikin akwai ayoyin suratu Bakarah daga aya ta 125 zuwa ta 132 wanda suka hada da batun gigni dakin ka’aba da Annabin Ibarahim da Dan sa Ismail As da kuma irin bayanin Rokon da Annabi Ibrahim yayi ga Ubangijinsa.
Domin Karin bayani sai A duba Littafai kamar haka Majma’ul Bayan da kuma Biharul Anwar.
Allah Ya Umarci A Rufe Kofofin Masallacin Madinah Ban Da Kofar Da Sayyidana Ali As Yake Shigowa
9 ga watan Zulhijjah shekara ta 2 bayan Hijrah. Manzon Allah SAWA bayan Hijrah zuwa madinah da kuma kafa tsarin Musulunci wanda yakasance afarkon ranekun da yaje madina ya gida Masallacin domin yazma wajen Ibadah ga Musulmai da kuma zama wajen tattaruwansu domin wadansu abubuwan na sharia wanda ya zamo Mutanan Makka da sukayi Hijra zuwa Madina basu da gidajen da zasu zauna sun kasance suna kwana acikin wannan masallacin ne bayan wani dan lokaci manzon Allah Saboda kiyaye lamurra na Musulunci da kuma girmama wurare masu tsarkin a Muslunci ya hanasu kwana aciki kuma yabada Umarni dasu ginawa kansu gidaje.
To su Muhajirai da akayi haka sai suka ginawa kawunanan su gidaje a gefen masallaci amma kowannen su ya yayi wata kofa da zata kaiga masallaci kai tsaye don nuna soyayyar su gashi masallacin kuma su samu saukin shige da ficen su zuwa masallaci da gidaddajinsu kuma surin ka riskar sallah Jamaa tare da manzon Allah SAWA cikin sauki sosai.
Sun zauna ahaka wasu yan Lokuta ba mai yawaba saiga Mala’ika Jibrail AS ya sauka yazowa da Manzon Rahama As wahayi da cewa Allah Subhanahu wataala yana son ya kasance Masallaci acikin tsafta ako da yaushe kuma yakasance Musulmai yayin shige da ficen su acikisa su kasance cikin tsafta da tsarki saboda haka koafofin da suka bude wanda suke kaisu ga masallaci banda Kofar Imam Ali As arufe su
Sai Manzon Allah SAWA ya bawa Babban Sahabin Nan nasa Wato Mu’az Bin Jabal umarni da ya sanar da hakan ga Musulmai yace dukkan kofofin da suka bude dake kaiwa masallaci su rufe su to sai sahabin nan ya isar da sakon Manzon Allah SAWA ga Sahabban sa daga cikin su akwai Abubakar Umar Usman Dalha Zubairi Abdurrahman Abbas DA Hamza dukansu kuma sukai biyayya ga wannan umarnin da aka basu suka rufe kofofin su. Amma wasu daga cikin su sunyi rokon abar masu koda gwargwadon ya kofa da zasu rinka hango abunda ke faruwa acikin masallacin amma Annnabi SAWA yace masu aa dole ne arufesu gaba daya kamar Yadda Umar yaje wajan sa aya bukaci hakan.
Hakan yasanya wasu daga cikin manyan Sahabbai Annabi AS da suke tare dashi sukaita korafi akai da labarه yaje ma Annabi SAWA wata rana ya tsaya a cikin masallacin Madina yayi masu Kuduba yana mai cewa labarin maganar da kuka fada dangane rufe kofofi yazo mani wallahi bani nayi haka ba Allah ne yayi domin Allah yayiwa Annabi musa AS Wahayi kan ya riki Masallacin amatsayin wuri mai tsarki ba wanda zaiyi Janaba acikin sa sai shi Musan da Harun da yayansa kawai haka nima Allah yamin wahayi dana riki wannan masallacin waje mai tsarki babu wandas zayyi janaba acikin sa saini da Ali Da yansa Alhasan da Husain As wallahi bani ne nayi umarini da rufe kofar Abubakar ba ko bude Kofar Ali Ba Allah ne ya umarceni da hakan.