Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban Bankin Akinwumi Adeshina ya ce akalla manoma miliyan 20 dake Afirka zasu amfana daga wannan shiri domin noma tan miliyan 30 na abinci iri iri da suka hada da alkama da masara da waken soya wadanda ake shigo dasu daga Ukraine.
Yanzu haka farashin abinci da takin zamani a Afirka sun tashi sakamakon mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine.
Yau Talata ne ake bude babban taron bankin na raya kasashen Afrika a birnin Acra na Ghana, bayan shafe shekaru biyu a jera ba’a gudanar ba sai ta kafar bidiyo sakamakon annobar korona.
342/