Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yayin taron manema labarai da ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka jagoranta ranar Laraba, sun tabo batutuwa da dama da suka shafi yankin.
Ministan harkokin waken Iraki, Fuad Hussein, ya yi fatan kasarsa za ta karbi sabon zagayen tattaunawa na tsakanin Iran da Saudiyya, bayan dakatar da tattauanwar na dan lokaci.
Game da batun Afganistan kuwa, Fuad Hussein, ya kuma bayyana cewa yana da ra’ayi guda da Iran kan cewa akwai bukatar kafa gwamnati wacce ta kunshi dukkan bangarori a Afghanistan domin samar da zaman lafiya.
Kan yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a Yemen kuwa bangarorin sun yi fatan ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin dake rikici domin samar da zaman lafiya maio daurewa.
342/