Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A Bana kungiyar tarayyar Afrika ta zabi taken wannan shekarar a matsayin shekarar tunawa da hadinkai da kuma sabuntawa da Jaddada aniyar da ake da shi na daukar tsauraren mataken hana sake afkuwar yakin kare dangin a nahiayr baki daya
A ranar 7 ga watan Aprilu ne shugaban kasar Ruanda Paul Kagame ya data fitala a birnin Kagali domin tunawa da kisan kare dangi da aka yi a kasar, inda sama da mutane 250.000 lamarin ya shafa, kuma za’a ci gaba da gudanar da bikin juyayin har zuwa ranar 13 ga watan Aprilu. Kuma za’a kwashe kawano 100 a na gudanar da tarurruka na tsawo kwanakin da aka kwashe ana tafka kisan kiyashin
A shekara ta 2021 ne shugaban kasar Faransa Emanual Makron ya ce kasar faransa ta taka rawa , amma bai ce a bangaren kisan kiyashin ba, shi ne shugaban kasa ko wani babban jami’I a na farko da ya taba furta hakan, inda aka ganinsa a matsayin daya daga cikin kisan kiyashi da aka yi mafi muni a zamanin nan.
342/