15 Faburairu 2022 - 16:22
Iran : Ana Murnar Zagayowar Ranar Haihuwar Iman Ali (a.s)

A Iran, an kwashe daren jiya ana bukukuwan murnar zagayowar ranar haihuwar Iman Ali (a.s).

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -An haifi Imam Ali, wanda shi ne mutum na farko da ya musulunta, sannan kuma surukin Manzon Allah mai girma, Muhammad ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da zuriyarsa), a ranar 13 ga watan Rajab (wata na bakwai na kalandar musulmi) kimanin shekara ta 600 a dakin Ka'aba da ke birnin Makka.

Haka nan Imam Ali (a.s) ya yi hidima wajen yada addinin Musulunci a duniya kuma ya shahara da juriya da kunya da jajircewa da kishin musulinci.

A Iran, mutane sun yi wa masallatai da gidaje da tituna da kantuna ado da kayan ado da fitulu masu launi tare da rarraba kayan zaki da alewa a matsayin wata hanya ta murnar zagayowar ranar haihuwar Imaminsu na farko.

Haka kuma ranar a Iran akan yi mata takan ranar mahaifi ko ta mazaje.

342/