29 Janairu 2022 - 19:56
​Mali: Masu Mulki Sun Gargadi Kasashe Waje Akan Tsoma Musu Baki A Harkokin Cikin Gida

Sojojin na kasar Mali sun ja kunnen kasashen Faransa da kuma Danmark da su dena yi wa siyasar kasar ta Mali shiga sharo ba shanu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kakakin gwamnatin sojan kasar ta Mali KAnar Abdullahi Maiga ya nemi ganin minister tsaron Faransa Florence Parly da ta daina Magana akan kasar ta Mali.

Maiga wanda ya bayyana hakan a wata hira ta kafar Talbijin ya yi watsi da zargin da ministar ta Faransa ta yi wa kasarsa da tsonaka a yankin Sahel.

Tun a cikin watan Ogusta na 2020 e da sojoji su ka kifar da gwamnatin Bubakar Keita, alaka a tsakanin Faransa da Malin ta yi kamari.

Mali da bukaci ganin sojojin Danmark da suke aiki a ciki kasar ta Mali da su fice, lamarin da haddasa sabani a tsakaninta da Faransa. Sojojin na Danmark da sun shiga cikin kasar Mali ne domin su taimakawa na kasar Faransa a karkashin farmakin da suke kira da Takuba.

342/