18 Janairu 2022 - 13:53
​Mali Ta Ce Faransa Ce Ke Bayan Matakan Da ECOWAS Ta Daukan Kanta

Gwamnatin rikon kwarya a Mali, ta ce faransa ce ke bayan dukkan matakan da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ta dauka kanta.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shugaban gwamnatin riko ta Mali ne, Chogel Maiga, ya bayyana hakan a wata doguwar hira da gidan talabijin din kasar ORTM.

Mali ta kuma sanar da shigar da kara kan takunkuman tattalin arziki da kungiyar ECOWAS da UEMOA, suka kakaba mata.

Ya kuma ce dukkan matakan da aka dauka an dauke su ne domin ruguza kasar ta Mali, da kuma al’ummarta da sun riga sun tagayyara, wanda a cewarsa duk Faransa ce ke bayan wannan yunkuri na wargaza kasar.

Game da zabubukan kasar, Chogel Maiga, ya goyi bayan samar da sauye sauye kafin gudanar da zaben domin kawo karshen cin hanci da rashawa, rashin adalci da kuma matsalar tsaro a kasar.

Firaministan riko na Malin, bai sanar da wani jadawalin zabe ba, amma ya ce kofarsu a bude take game da duk wata tattaunawa da kungiyar ecowas.

342/