Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Jaridar Egypt today ta kara da cewa girgizan kasar mai ma’aunin Richter 5.4 ta awkawa tsibiran Cassos da Crete na kasar Girka ne a ranar litinin, sannan wata mai ma’aunin richter 5.2 ta sake aukawa tsibirin Crete, sa’o’i 4 bayan ta farkon, wanda ya kai ga wasu mazauna bakin Tekun Medeteranian a kasar Masar sun ji kararta.
Magajin garin tsibirin Cassos wanda yake kusa da inda abin ya auku ya bayyanawa kafafen yada labarai a birnin Athens babban birnin kasar Girkaka kan cewa girgizan kasar bata jawo wata asara ko ta ginegine ko ta rayuka ba.
342/