ABNA24 : Bangarorin sun tattauna kan batutuwan da suka shafi alakar dake tsakanin kasashen biyu, dama batutuwan da suka shafi yankin dama kasa da kasa.
Kamfanin dilancin labaren ISNA na Iran, wanda ya rawaito labarin, ya bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar ta Iraki, zai mikawa hukumomin kasar Iran, wasikar gayyata a taron kasa da kasa da za’a gudanar kan kasar Iraki.
A karshen watan nan ne ake sa ran Iraki, za ta shirya taron wanda zai hada wasu kasashen yankin da na yamma.
342/