4 Afirilu 2021 - 06:41
Iran Da Iraƙi Za Su Ci Gaba Da Bin Lamarin Kisan Gillan Da Amurka Ta Yi Wa Janar Sulaimani

Babban sakataren majalisar ƙoli ta kare haƙƙoƙin bil’adama ta ƙasar Iran Dr. Ali Baƙeri Kani ya bayyana cewar kwamitin haɗin gwiwa da Iran da ƙasar Iraƙi suka kafa zai ci gaba da bin lamarin kisan gillan da Amurka ta yi wa tsohon kwamandan dakarun Кudus na ƙasar Iran, Laftanar Janar Кasim Sulaimani.

ABNA24 : Dr. Kani ya bayyana hakan ne a wata hira a yayi da manema labarai inda ya ce: Tuni sun fara gudanar da wani shiri tare da haɗin gwiwan Iraƙawa, waɗanda suke da haƙƙi da kuma ikon ci gaba da bin wannan ɗanyen aiki saboda ya faru ne a cikin ƙasar su sannan kuma an kashe musu ‘yan ƙasar su.

Babban sakataren majalisar ƙoli ta kare haƙƙoƙin bil’adama ta ƙasar Iran ya ce tunin ofishin mai shigar da ƙara kan laifuffuka na ƙasa da ƙasa, wanda shi ne ke da alhakin wannan lamarin, yana matakin ƙarshe na tsara ƙara da kuma zargin da ake yi wa waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.

A ranar 3 ga watan Janairun 2020 ne sojojin Amurka bisa umurnin tsohon shugaban ƙasar Donald Trump suka kashe Janar Кasim Sulaimani, tare da mataimakin dakarun sa kai na ƙasar Iraƙin Abu Mahdi Al-Muhandis a kusa da filin jirgin saman Bagadaza.

342/