ABNA24 : Jadakan na Iran a Yemen ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zatawa da ministan harkokin wajen gwamnatin san’a, inda ya bayyana masa cewa, kawo karshen wannan rikici ta hanyar fahimtar juna tsakanin dukaknin bangarorin siyasa da al’umma a kasar Yemen ba tare da shigar shugula ta kasashen ketare ba, hakan shi ne mafita.
Shi ma a nasa bangaren ministan harkokin wajen Yemen na gwamnatin San’a Hesham Sharaf Abdullah ya bayyana cewa, suna goyon bayan duk wani mataki da zai taimaka wajen kawo karshen yakin da makiya kasar Yemen suke kaddamarwa a kanta.
Ya ce kawo karshen yakin ya hada da kawo karshen killace kasar da makiya suke yi, da kuma gaggauta bude filin sauka da tashin jiragen sama na San’a, domin damar shigo da kayayyakin da al’ummar kasar suke bukata cikin gaggawa.
Baya ga haka kuma bangarorin biyu sun tattauna kan sakamakon ziyarar da manzon musamman na majalisar dinkin duniya mai shiga tsakani kan rikicin kasar Yemen Martin Griffiths ya kai kasar Iran, da kuma abubuwan da ya tattauna a kansu tare da jami’an gwamnatin kasar ta Iran, kan hanyoyin warware matsalar kasar ta Yemen.
342/