ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar 120 ne suka halarci wani taro ta yanar gizo a makon da ya gabata don tattauna batun kafa sabuwar jam’iyya ta Republican.
Wasu yan jam’iyyar guda 4, wadanda kuma suka halarci taron sun bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya mamaye al-amura a jam’iyyar ta yadda ba zasu iya aiki da shi ba. Sun kuma kara da cewa jam’iyyar za ta kalubalanci Donal Trump saboda zagon kasa da yake yiwa jam’iyyar.
‘Yan jam’iyyar da za su balle dai sun hada da tsoffin wadanda suke rike manya-manyan mukamai a kasar da kuma wadanda suke rike da mukamai a halin yanzu. Daga cikinsu dai akwai George H.W. Bush babba, George W. Bush karami da kuma Ronald Reagan dukkaninsu tsoffin shuwagabannin kasar.
342/