21 Janairu 2021 - 18:10
Iran: Gwamnan Babbam Bankin Iran Ya Ce An Sakewa Kasar Wasu Kudadenta Da Aka Tsare A Kasashen Waje

Gwamnan babban bankin kasar Iran Abdonnasir Himmati ya bayyana cewa gwamnatin kasar Korea ta Kudu ta saki wasu daga cikin kudaden kasar wadanda ta tsare saboda biyayya ga takunkuman gwamnatin kasar Amurka kan kasar.

ABNA24 : Tashar Talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Himmati yana fadar haka a yau Laraba bayan taron majalisar ministocin kasar a nan birnin Tehran.

Himmati bai bayyana yawan kudaden kasar da aka mayar mata ba, amma banki Millit na kasar Iran da ke birnin Seul babban birnin kasar Korea ta kudu kadai ya na da dalar Amurka biliyon $2.7, a yayinda bakin ‘Industerial Bank of Korea kuma yake tsare da dalar Amurka biliyon 7 na kasar.

Mafi yawan wadannan kudade dai na sayen danyen man fetur ne daga kasar Iran kafin takunkuman tattalin arziki mafi muni wadanda gwamnatin Amurka ta dorawa kasar.

Himmati ya kammala da cewa gwamnatin kasar tana kokarin ganin an saki dukkan kudaden kasar wadanda suke tsare a bankunan kasashen waje.

342/