ABNA24 : Hukumar agajin gaggawa ta jahar ta Bauchi ta tabbatar da afkuwar lamarin a cikin kananan hukumomi daban-daban na fadin jahar.
Sakataren hukumar ta SEMA, Habu Ningi ya bayyana cewa; mun ziyarci dukkanin yankunan da lamarin ya faru, kuma mun sami rahotanni daga kananan hukumomi 11 a fadin jahar.”
A jahar Niger, ambaliyar ruwan ta nutsar da gidanen da su ka kai 50, da kuma barnata dukiyar da ta kai miliyoyin nairori, musamman a yankin Gallah, a karamar hukumar Agwara.
Dan majalisar wakilai daga yankin Borgu-Agwara a majalisar kasa, Alhaji Jafaru Muhammadi ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis, bayan da ya gana da wadanda lamarin ya rutsa da su.
A jahar Kebbi ma an sami ambaliyar ruwan wacce ta mamaye hanyoyi da gidajen mutane.
342/