18 Yuli 2020 - 11:29
​ Mali : ECOWAS Ta Shawarci Bangarorin Dake Bore Su Shiga Gwamnatin Hadin Kai

Kwararun kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, dake neman sasanta rikicin kasar Mali, sun shawarci bangarorin dake zanga zanga a kasar dasu shiga a dama dasu a gwamnatin hadin kan kasa.

ABNA24: Tawagar ta Ecowas da ‘yan adawan a kasar ta Mali, sun gana a karo na hudu, tun bayan da tawagar ta sanya kafarta a kasar.

A cewar kwararun na ECOWAS, shigar ‘yan adawan a dama dasu zai taimaka sosai wajen shawo kan rikicin kasar da kuma zakulo duk wadanda suke da hannu a kisan fararen hula yayin zanga zangar baya bayan nan.

A wani lokaci yau Asabar ne ake sa ran tawagar kungiyar ta ECOWAS, zatayi wa ‘yan jarida bayyani game da ganawar data yi da dukkan masu da tsaki kan rikicin kasar ta Mali.

342/