(ABNA24.com) Shugaban Kungiyar Ansarullah Ta Kasar Yemen Ya Bayyana Cewa; Imani Shi ne Ginshikin karfin Da Su Ke Da Shi Wajen Fuskantar Makiya
Sayyid Abdulmalik Badruddin al-Huthy ya bayyana cewa; “Yancin da al’ummar Yemen suke so, shi ne cikakken ‘yanci wanda bai tattare da yin biyayya ga wata kasa.
Shugaban kungiyar ta “Ansarullah” ya kuma kara da cewa; Tushen karfin da al’ummar Yemen suke da shi, shi ne rikonsu da imani, shi ne yake ba su karfin soja da kuma jajurcewarsu.
Abdulmalik al-Huthy ta kara da cewa; tsohuwar gwamnatin kasar ta kasance mai yin biyayya ga Amurka, amma kuma a lokaci guda babu wani ‘yanci da Amurkan ta ba ta.
Har ila yau, Abdulmalik Huthy ya yi ishara da yadda kasar ta kasance cikin rashin tsaro da tashe-tashen hankula da koma baya na tattalin arziki ta yadda kasar ta fuskanci durkushewa.
/129
2 Maris 2020 - 07:47
News ID: 1014302

Shugaban Kungiyar Ansarullah Ta Kasar Yemen Ya Bayyana Cewa; Imani Shi ne Ginshikin karfin Da Su Ke Da Shi Wajen Fuskantar Makiya