tsamarin rashin tsaro a Najeriya

  • Najeriya: Sama da Masallata 60 Ne Aka Sace

    Najeriya: Sama da Masallata 60 Ne Aka Sace

    An sace masu salla sama da 60 a harin da wasu mutane dauke da makamai suka kai kan babban masallacin garin Dakara a jihar Neja ta Najeriya. Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da ake gudanar da sallar Juma'a, kuma maharan bayan sun yi ta harbe-harbe kwatsam, suka fitar da wasu masu salla daga masallacin suka tafi da su zuwa daji.