Bankin Duniya, a cikin rahotonsa na ‘Africa Pulse’ na watanni shida, ya daga hasashen ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka kudu da hamadar Sahara daga kashi 3.5 cikin 100 a rahoton da ya gabata a watan Afrilu zuwa kashi 3.8 bisa 100, bisa dalilai da suka hada da raguwar hauhawar farashin kayayyaki, daidaita darajar kudin waje, da kara zuba jari a manyan kasashe masu karfin tattalin arzikin yankin kamar Habasha, Najeriya, da Ivory Coast.